Latest:
Labarai

Masu kwacen katin ATM sun shiga hannun ƴan Sanda a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kama wasu mutum biyu bisa zargin kwace wa mutane katin cirar kudi na ATM.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Mohammed Jalige ya fitar, ya ce rundunar ta kama mutanen ne bayan samun rahoto daga wata mata da aka ƙwace wa katin na ATM.

Matar ta bayar da rahoton cewa a lokacin da ta je banki domin cirar kuɗi, sai wani mutum ya zo da nufin taimaka mata, daga nan ya musanya mata katin nata.

Mintuna bayan haka, sai aka tura wa matar saƙon cirar kuɗi har naira 404,000 daga asusun ajiyar bankin nata.

Sanarwar ta ce bayan zurfafa bincike ne jami’an sashen tattara bayanan sirri suka kama wasu mutum biyu, Paul Agu Daniel, da Mike Ogah, kuma duka sun amsa laifin da ake tuhumar su da shi.

Binciken jami’an tsaron ya kuma gano cewa mutanen biyu sun sace wa wani mutum kuɗin da ya kai naira 948,000 ta hanyar amfani da katinsa na bankin Fidelity da suka sace.

‘Yan sandan sun ce a halin yanzu mutanen biyu na hannunsu domin ci gaba da gudanar da bincike.

Sanarwar ta kuma ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ya yaba wa jami’an tsaron sashen tattara bayanan sirrin kan kama mutanen.

Sannan ya yi kira ga jama’a da su riƙa lura da irin mutanen da za su bai wa katinan ATM ɗinsu domin taimaka musu.

BBC Hausa

Leave a Reply