Latest:
Labarai

Matashin Da Ya Yi Wa ‘Yar Shekara 10 Fyade A Jihar Bauchi

 

Ana zargin matashi mai shekara 33 da yin amfani da sinadarin saka maye wajen gusar da hankalin karamar yarinya ‘yar shekara 10, tare da yi mata fyade a karamar hukumar Ningi dake jihar Bauchi.

Matashin ya yaudari yarinyar ne ta hanyar ba ta lemo da ake zargin na dauke da sinadarin saka mayen don ya samun damar yin lalata da ita ba tare da saninta ba.

Cikin wata sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar, ya ce, wanda ake zargin ya samu damar yi wa yarinyar fyade ne ta hanyar nuna karfi.

Ya ce, “A ranar 25 ga watan Mayun 2023, wani mutum da ke kauyen Nasaru a karamar hukumar Ningi ya kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda a Ningi, inda ya ce wani matashi da suke gari daya ya yaudari ‘yarsa mai shekara 10 ta hanyar ba ta lemo da ake zargin na dauke da sinadarin saka maye wanda hakan ya yi sanadin gushewar hankalin ta.

“Ya yi amfani da wannan damar ya yi mata fyade, wanda ya hakan ya sanya yariyar ta gamu da raunuka a al’aurarta kana ta yi ta zubar da jini.”

Sanarwar ta kara da cewa, tun lokacin da suka amshi rahoton, tawagarsu cikin hanzari ta garzaya inda lamarin ya faru tare da daukar yarinyar zuwa babban asibitin Ningi, inda daga bisani aka maida ta asibitin kula da masu yoyon fitsari (NOFIC) da ke Ningi, nan ma suka sake tura ta zuwa asibitin gwamnatin tarayya (FMC) da ke Birnin Kudu a jihar Jigawa domin karin kulawar likitoci.

A cewar Wakil, tun a lokacin ‘yan sanda suka sha alwashin kamo wanda ya aikata hakan domin tabbatar da cewa anyi ma yarinyar adalci, “wanda a lokacin ma mun cafke wanda ake zargi, mai suna Danladi Ibrahim.

“A lokacin da ake tuhumarsa, ya amsa da kansa cewa ya aikata laifin, don haka bincike na cigaba da guduna kuma da zarar an kammala za mu gurfanar da shi a gaban kuliya manta sabo.”

Daga karshe kuma rundunar ‘yan sandan ta ja hankalin al’umma da su rika sanya ido da lura da yankunansu domin dakile aniyar bata gari a kowani lokaci tare da gaggawar kai rahoton faruwar lamuran da basu dace ba cikin hanzari domin daukan matakan gaggawa.

Leave a Reply