Home Labarai Ministan Tsaro Da Sakataren Gwamnatin Chadi Sun Ajiye Aikinsu kan Bidiyon Batsa

Ministan Tsaro Da Sakataren Gwamnatin Chadi Sun Ajiye Aikinsu kan Bidiyon Batsa

Ministan Tsaron Chadi, Daoud Ibrahim da Sakataren Gwamnatin Kasar, Haliki Choua Mahamat, sun ajiye ayyukansu bayan fitar wasu bidiyoyinsu na batsala guda biyu.

Rahotanni sun ce jami’an gwamnatin sun ajiye aikin nasu ne a ranar Laraba, bayan bidiyoyin nasu sun karade gari musamman a kafafen sada zumunta na zamani.

Kakakin Firaministan kasar, Saleh Kebzabo ne ya ce gwamnatin ta amince da ajiye aikin nasu, kodayake sanarwar ba ta yi cikakken bayani ba.

Bidiyoyin dai da aka yada a ranakun Lahadi da Litinin, sun nuna mukarraban gwamnatin suna mu’amala da wasu.

Sai dai kamfanin dillancin labarai na Reuters bai iya tabbatar da sahihancin bidiyoyin ko jin ta bakin tsofaffin jami’an gwamnatin domin su mayar da martani a kai ba.

Ba kasafai dai ake samun badakalar fitar bidiyoyin batsa ba a Chadi, wacce galibin ’yan kasar Musulmai ne.

NAN/Jaridar Aminiya


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.