Gwamna Dauda Lawal, ya mayar da martani ga Ministan Labarai, Mohammed Malagi kan batun sulhun da ake yi cikin sirri da âyan bindiga.
Ya ce Gwamnatin Zamfara tana da gamsassun hujjoji da ke fallasa wasu jamiâan Gwamnatin Tarayya da hannu dumu-dumu a shirya zaman sulhu da âyan bindiga.
A jiya ne Ministan na Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Malagi ya zargi Gwamnatin Zamfara da siyasantar da lamarin tsaro. Biyo bayan neman Æarin bayani da Gwamna Dauda ya yi kan zargin zaman sulhu ta ÆarÆashin Æasa da âyan bindiga.
A wata takardar manema labarai, mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa Gwamnatin Dauda Lawal tana da hujjoji masu tayar da hankali da ke fallasa wasu jamiâan Gwamnatin Tarayya kan sulhu da âyan bindiga.
Ya Æara da cewa Ministan na Labarai ya yi ri-ga mallam masallaci wurin yanke hukunci tare da yankewa gwamnatin Zamfara hanzari.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: âMun nemi Æarin bayani daga Gwamnatin Tarayya kan zaman sirri na sulhu da wasu jamiâanta suke jagoranta a Zamfara ba tare da sanin Gwamnatin Jiha ko shugabanni jamiâan tsaron jihar ba.
âMuna da gamsassun hujjoji dake tabbatar da wannan zaman sulhu tsakanin jamiâan Gwamnatin Tarayya da âyan bindiga a wurare mabambanta a Zamfara.
âAkwai ban takaici a ce Ministan YaÉa Labarai zai fito bainar jamaâa ya kore batun ba tare da ya nemi sani daga jamiâan tsaro ko âyan uwanshi da ke da hannu dumu â dumu a lamarin ba. Mun tsammaci tunda Æwararre ne a harka watsa labarai, zai bi matakan da ilimi ya sharÉanta don tabbatarwa ko kore batun namu.
âGwamnatin Jihar Zamfara tana matuÆar mutunta Æaâida tare da ganin Æimar hukuma. Ba za mu fito kafafen watsa labarai muna fallasa sunayen jamiâan Gwamnatin Tarayyan da ke wannan taâasa ba, amma mun sanar da âyan Nijeriya don su nemi Æarin bayani daga Gwamnatin ta Tarayya.
âMuna so mu sanar da Minista cewa jamiâansu na Gwamnatin Tarayya da ke jagorantar wannan zaman sulhu da âyan bindiga, sune ke siyasantar da matsalar tsaro, ba Gwamnatin Zamfara ba.
âBa mu san daga inda Ministan ya samu Æwarin gwiwan bugun Æirji ya ce babu wani zaman sulhu da aka yi a Zamfara ba, saboda ai mun bayyana wuraren da aka yi waÉannan zama, irinsu Birnin Magaji, Maradun, Mun Haye, Ajah, Bawo, da kuma Bagege.
âMuna sake nanatawa cewa sulhu da âyan bindiga a Zamfara ba zai taÉa haifar da Éa mai ido ba. Sam! Ba wannan ba ne mafita ga matsalar, a yi amfani da qarfi kawai a kauda su, wanna ita ce matsayarmu har gobe.
âMuna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta daina biye wa âyan amshin Shata, ta yi bincike tare da wanke kanta daga aikin waÉannan dillalan sulhu da âyan bindiga.â In ji shi.
Jaridar Leadership
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.









