Majalisar dattijan Najeriya ta ce za ta cigaba da shiga tsakanin kan dambarwar zarge-zargen da ake yiwa alkalin alkalai mai murabus, Mai Shari’a Tanko Muhammad, da wasu alkalan kotun koli ke yi duk da cewa ya yi murabus.
A ranar Lahadi, Mai Shari’a Muhammad ya ajiye aikinsa na alkalin alkalai, kan dalilan na rashin lafiya, kuma tuni aka maye gurbinsa da mutumin na biyu mafi mukami a kotun koli, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola.
Alkalai 14 na kotun koli ne suka shigar da korafi kan tsohon alkalin alkalan, su na zarginsa da yi biris da hakokinsu, da kin sanyasu a harkokin kotun, wanda hakan ya sake dagula harkokin kotun da kuma tasiri a shari’o’i.
Amma Mai shari’a Muhammad ya musanta waɗannan zarge-zarge da yin alla-wadai da fitar da maganar ga al’ummah.
Duk da cewa alkalin alkalan ya yi murabus, majalisa, bayan kudiri da aka gabatar gabanta a ranar Talata, ta bukaci kwamitin ta cigaba da bincikenta da kuma samar da maslaha kan dambarwar.
Majalisar ta bukaci kwamitin ya tattauna da masu ruwa da tsaki domin nazartar korafe-korafen da alkalan kotun koli suka gabatar.
Masu ruwa da tsakin za su kasance daga kowanne bangarori uku na gwamnati.
Majalisar ta kuma yi addu’a samun lafiya ga alkalin alkalan mai murabus.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.