Labarai

Za Mu Hana Rasha Nasara A Yaki Da Ukraine – G7

Shugabannin ƙasashen G7 masu karfin tattalin arziki a duniya sun ce za su tsaurara matakan hana wa kasar Rasha cin ribar yaƙin da ta ƙaddamar a kasar Ukraine.

A karshen taron da suka gudanar a  kasar Jamus, shugaban kasar Jamus Olaf Scholz, ya ce shugaba Putin ba zai yi nasara ba kuma G7 za su ci gaba da zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

Ya ce “mun amince cewa Shugaba Putin ba zai taɓa yin nasara ba a wannan yaƙi, za mu matsa mu cije.

Ya kuma ce za su yi ƙoƙarn magance tsadar albarkattun mai da yakin Rasha ya haddasa, wanda ya jefa ƙasashen cikin rashin tabbas.

Ƙasashen sun kuma ce za su kara dala biliyan huɗu da rabi wajen yaƙi da yunwa a duniya – matsalar da ta yi muni sakamakon yaƙin Rasha da Ukrain.

Matakan sun haɗa da ba manoman Ukraine tallafi da magance ƙarancin taki da kuma samar da mafitar fitar da kayayaki a Bahar Aswad.

Leave a Reply