Home Labarai NDLEA ta kama mutane 372 masu safarar miyagun kwayoyi a Bauchi

NDLEA ta kama mutane 372 masu safarar miyagun kwayoyi a Bauchi

Daga Ude Israel

Hukumar yaki da hanasha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa NDLEA reshen jihar Bauchi ta ce ta kama mutane dari uku da saba’in da biyu masu safarar muggan kwayoyi tare da gurfanar da 103 daga cikin su gaban kuliya, a yayinda ake cigabada gudanar da shari’o’i 31 a gaban kotu, kana kuma 73 aka ba su shawara tare da sauya musu ɗabi’unsu.

Kwamandan hukumar ta NDLEA a jiha Ali Aminu ne ya bayyana hakan a wannan Litinin a yayin wata ganawa da manema labarai a ofishinsa wanda hakan yazo daidai da bikin ranar yaki da hanasha da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya na shekarar 2023.

A cewarsa, rundunar tare da hadin gwiwar rundunar soji 33 Artillery sun gano tare da girbe gonar da ake noman tabar wiwi a kauyen Digari da ke karamar hukumar Alkaleri ta jihar.

Sauran wuraren da aka gano gonakin tabar wiwi a jihar a cewarsa sun hada da kauyen Dafa Tuwo dake cikin karamar hukumar Darazo, Tsangayar Njeri a karamar hukumar Ningi da kuma garin Giade dake karamar hukumar Giade.

Ya kara da cewa tun daga lokacin da ya shiga ofis a watan Agustan 2022 zuwa yanzu, sun kama sama da kilogiram dubu daya na nau’ukan magunguna daban-daban.

Ya kuma nuna rashin jin daɗinsa a bisa nuna kyama a cikin al’umma da masu shaye-shayen miyagun kwayoyi ke fuskanta wanda a cewarsa hakan na kashe musu gwiwa wajen neman magani, inda ya ce hakan na kuma yin illa ga zamantakewa da tattalin arzikin daidaikun mutane da iyalansu.

Kwamandan NDLEA na jihar ya ce kalubalen kayan aiki daga cikin babban kalubalen da ke fuskantar rundunar , tare kuma da yaba wa Gwamna Bala Mohammed a bisa sha’awar sa na ganin an rage shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar tare da yin kira da a kara ba da tallafi a fannin kayan aiki.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.