Zababban shugaban Kenya William Ruto, da babban abokin takararsa a zaben baya bayannan Raila Odinga, zasu gana da sanatan Amurka Chris Coon, wanda ke ziyara a kasashen Afirka biyar.
Har yanzu Amurka bata taya mista Ruto murnar samun nasara ba bayan an ayyana shi a hukumance cewa ya samu nasara a zaben da mr Odina ya ce bai amince dashi ba.
Kazalika sanata Chris, da tawagarsa zasu gana da shugaba Uhuru Kenyatta.
A ranar Laraba ce sanatan ya isa Nairobi, babban birnin kasar, doni tattauna wa da shugabannin uku a kan batun lafiya da tsaro da kuma tattalin arziki.
Tuni dai rahotanni suka ce sanatan ya gana da mr Ruto in da suka tattauna a kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Haka kuma tawagar sanatan za ta gana da masu ra’ayin ‘yan mazan jiya da jami’an lafiya da kuma kungiyoyin da ke aiki don samar wa mata ayyukanyi a kasar.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.