Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Sanata George Akume a matsayin sabon sakataren gwamnatin tarayyar ƙasar.
An yi bikin rantsarwar ne a gaban jami’an gwamnatin ƙasar a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Laraba da safe.
Daga cikin waɗanda suka halarci rantsar da sabon sakataren gwamnatin sun haɗar da mataimakin shugaban Najeriya Sanata Kashim Shettima, da shugaban majalisar dattawan ƙasar Sanata Ahmad Lawan da gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq da shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya Dakta FolasadeYemi-Esan.
A makon da ya gabata ne sabon shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya sanar da naɗin George Akume da Femi Gbajabiamila a matsayin sakataren gwamnatin tarayya da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati.
BBC Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.