Babban mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya ce matsalar satar danyen man fetur ce ta kara tsadar rayuwa a kasar.
Malam Nuhu Ribadu ya fadi haka ne yayin cewa Najeriya na asarar gangar danyen mai 400,000 duk rana sakamakon ayyukan Éarayin man na ciki da wajen Æasar, duk kuwa da ÆoÆarin da gwamnati ke yi na kawar da matsalar Éarayin man.
Ribadu ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci tawagar da shugaban Æasa ya aike zuwa duba wasu wurare na man fetur da iskar gas a yankin Owaza na Jihar Abiya da kuma Odogwa na Karamar Hukumar Etche da ke Jihar Ribas.
Da yake jawabi a gaban manema labarai a ranar Asabar, Ribadu ya ce ayyukan masu satar Éanyen mai da ke fasa bututan mai na kawo wa Æasar babban naÆasu ta fuskar tattalin arziki, lamarin da ya ce shi ke haifar da tsadar rayuwa a Æasar.
âAbin takaici ne yadda wasu tsirarun mutane ke sace albarkatun Æasarmu domin amfanar da kawunansu, abin da kuma ke haifar da asara mai yawa ga Æasarmu da mutanen yankin.â
Ya Æara da cewa âNajeriya na da arzikin man da za ta iya haÆo gangar mai miliyan biyu a kowacce rana, amma yanzu Æasa da ganga miliyan 1.6 kawai muke iya haÆowa, sakamakon ayyukan Éarayin mai da masu fasa bututan man.â
âKenan kusan gangar mai 400,000 wasu Éata-gari da masu yi wa tattalin arzikinmu zagon-Æasa ke sacewa a kowacce rana domin amfanar da kansu,â in ji Ribadu.
Mai bai wa shugaban Æasar shawara kan harkar tsaro ya ce darajar gangar mai 400,000 a yanzu ta kai dala miliyan hudu, âkenan waÉannan kuÉaÉe muke asara a kowacce rana sakamakon ayyukan waÉannan Éata-garin.â
âIdan ka lissafa dala miliyan huÉu sau kwanakin shekara 365, za ka ga cewa maÆudan biliyoyin daloli muke asara a kowacce shekara.â
KuÉin da ya ce sun isa Æasar inganta tattalin arzikinta ta hanyar farfaÉo da darajar Æudin Æasar, da rage tsadar rayuwa da sauran fannoni.
Ribadu ya Æara da cewa gwamnatin Shugaba Tinubu na damuwa da wannan mummunar Éabiâa, ya kuma ce gwamnatin ta fara Éaukar matakai don kawo Æarshen wannan matsala.
Jaridar Aminiya
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








