Shugaban Ma’aikatan Kano, Alhaji Usman Bala ya yi murabus daga muƙaminsa.
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Kano, Dokta Abdullahi Baffa Bichi ya sanar a wannan Larabar.
Sanarwar ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci Babbar Sakatariyar Hukumar Ma’aikatan, Hajiya Ma’azatu Isa Dutse ta ci gaba da lura da ayyukan Ofishin har zuwa lokacin da za a naɗa magajinsa.
Ana iya tuna cewa, a watan Afrilun 2022 ne tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Alhaji Bala a matsayin Shugaban Ma’aikatan na Kano
Wata guda da yi masa naɗin, Ganduje ya sake daga likafar Alhaji Bala, inda ya kara masa da mukamin Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Kano.
Jaridar Aminiya
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.