Latest:
Labarai

Sojojin Nijeriya sun kashe ƴan Boko Haram 23 a Borno

Sojojin Nijeriya sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram akalla 23 a wani hari da suka kai musu a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Daraktan watsa labarai na rundunar sojin kasar Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a wata sanara da ya fitar ranar Asabar.

Ya ce mayakan kungiyar da dama sun tsere dauke da muggan raunuka a yayin da rundunarsa ke ci gaba da fatattakarsu.

Janar Buba ya kara da cewa sun kubutar da mutum 41 da mayakan kungiyar suka yi garkuwa da su, kana sun kwato tarin makamai daga wurinsu.

Hakan na faruwa ne kwanaki kadan bayan kungiyar Boko Haram ta saki mata 49 da ta sace a Shuwaei Kawuri da ke jihar ta Borno bayan an biya kudin fansa.

Tun shekarar 2009 dakarun Nijeriya suke fafatawa da mayakan kungiyar Boko Haram wadanda suka kaddamar da yaki kan kasar.

Alkaluman hukumomi sun nuna cewa ‘yan kungiyar sun kashe fiye da mutum 100,000, da suka hada da fararen-hula da jami’an tsaro a shekaru 14 da suka gabata.

TRT Afrika Hausa

Leave a Reply