Labarai

Sojojin sun kuɓutar da tsohon shugaban kwalejin ilimi da ɗansa a Zamfara

 

Rundunr sojin Najeriya ta ce kubutar da tsohon shugaban kwalejin ilimi ta tarayya da ke Gusau Dakta Hassan Abubakar Augie tare da ɗansa daga hannun masu garkuwa da mutane.

Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a shafinsa na Tuwita, sun dakarunsu na rundunar Hadarin Daji da ke Mada ne suka kubutar da Dakta Augie tare da ɗansa a lokacin wani sintiri da suka gudanar da a kan hanyar Shemori zuwa Yandoto.

Sanarwar ta ce dakarun sun fatattaki ‘ayn bindigar masu yawa, inda suka yi musayar wutar da su.

Sojojin sun ce ‘yan bindigar sun gudu zuwa cikin daji bayan da suka ji wuta daga ɓagaren sojojin, tare da barin mutanen biyu da suka sacen..

Binciken farko ya nuna cewa an sace mutanen biyu ne a daren ranar Alhamis a gidan Dakta Augie, inda aka tafi daji da su inda suka ci gaba da tsare su, har zuwa lokacin da sojojin suka isa wajen.

Sojojin sun kuma samu nasarar ƙwato babura biyu na ‘yan bingidar a lokacin gumurzun.

Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da rikice-rikicen ‘yan bindiga da ke sace mutane domin neman kudin fansa.

BBC Hausa

Leave a Reply