Latest:
Labarai

Nnamdi Kanu Ya Kalubalanci Shari’ar Da Ake Masa

Jagoran kungiyar ‘yan aware ta IPOB a kudu maso gabashin Najeriya ya shigar da kara a watan kotun tarayyar kasar yana neman ta soke wani umarni da bangaren shari’a ya fitar a farko wannan watan da ke cewa za a daina sauraren dukkan shari’u na ta’addanci a bainar jama’a.

Nnamdi Kanu ya sanar da kotun ta hanyar lauyoyinsa cewa umarnin ya taka tsarin mulki da wasu dokokin kasar kuma ya kamata ta soke shi.

A ranar 8 ga watan nan ne mai shari’a John Terhemba Tsoho ya bayar da umarnin daina sauraren shari’un da ke da alaka da ta’addanci a bainar jama’a domin kiyaye tsaron dukan wadanda ke da alaka da shari’ar.

Alkalin ya hana ‘yan jarida halartar zaman kotunan da ke sauraren irin wadannan shari’un.

Baya ga alkalin da zai saurari shari’ar, mutanen da aka amince musu shiga dakin shari’ar su hada da wasu zababbun ma’aikatan kotun da jami’an tsaro.

Mista Kanu ya musanta aikata wani alifi.

Leave a Reply