Yan sanda sun cafke wasu Æarin likitoci biyu kan zargin haÉa baki da sace Æodar wani mara lafiya a Jos, babban birnin Jihar Filato.
Ana zargin likitocin biyu ne da haÉa baki da kuma aiki tare da wani Dokta Noah Kekere na Asibitin Murna da ke garin Jos, wajen cire Æodar wani mara lafiya mai suna Kehinde Kamal.
Kakakin rundunar âyan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya shaida wa âyan jarida cewa ana gudanar da bincike a kan waÉanda ake zargin.
A cewarsa, Kwamishinan âyan sandan jihar ya kafa kwamitin Æwararrun likitoci domin gudanar da bincike su gano gaskiyar zargin cire Æodar mara lafiyan.
A cewar kakakin âyan sandan, runduna ta kuma gano cewa Noah Kekere ba likita ba ne, kamar yadda yake gabatar da kansa.
Jaridar Aminiya
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.









