Fitaccen dan siyarar nan na Najeriya, Sanata Dino Melaye, ya bayyana amincewarsa da shan kaye a zaben fitar da gwani na dan majalisar dattawan Yammacin Kogi jam’iyyarsu ta PDP a Jihar Kogi da ke tsakiyar kasar.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, tsohon dan majalisar dattawan, ya amince da shan kaye a hannun wani dan siyasa Honorabul T.J. Yusuf sannan ya gode wa masu kada kuri’a.
Sai dai ya yi zargin cewa “taron-dangin” da aka yi masa yana da girma amma dai “ina godiya ga Allah.”
Sanata Melaye dai yana daga cikin na gaba-gaba wajen neman ganin jam’iyyar PDP ta tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin dan takararta a zaben 2023.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.