Home Labarai Tinubu ya aiyana wa Majalisar Dokoki shirin tura dakaru zuwa Nijar

Tinubu ya aiyana wa Majalisar Dokoki shirin tura dakaru zuwa Nijar

 

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya shaida wa majalisar dokokin Najeriya matsayar da ƙungiyar Ecowas ta cimma kan ɗaukar matakin soji a kan Nijar da kuma sauran takunkuman da aka ɗauka na ladabtar da sojojin da suka yi juyin mulki.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio ya sanar da saƙon shugaban ƙasar inda ya karanto kai tsaye daga wasikar shugaba Tinubun.

Wasikar na cewa “Bayan abin takaicin da ya faru a Nijar inda aka hamɓarar da shugaban ƙasa, Ecowas a ƙarƙashin jagorancina ta yi Allah-wadai da juyin mulkin kuma ta amince da ɗaukar matakan dawo da Nijar kan turbar dimokuraɗiyya. A wani mataki na dawo da zaman lafiya a ƙasar Ecowas ta fitar da matsaya.

“Za a rufe duk iyakokin Nijar da ƙasashenmu da kuma sanya ido don tabbatar da cewa an yi biyayya ga matakin.

“Yanke wutar lantarkin da ake kaiwa Nijar da neman goyon bayan ƙasashen duniya wajen aiwatar da matsayar ƙungiyar Ecowas da kuma datse sufurin jirgin sama daga cikin Nijar da ma wanda zai shiga ƙasar.

“Rufe hanyoyin shigar da kaya Nijar daga Legas da kuma wayar da kan ƴan Najeriya musamman a kafafen sada zumunta game da shirin ɗaukar matakin soji a kan sojojin Nijar ɗin.”

BBC Hausa


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.