Labarai

Shugabannin NNPP sun bukaci Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar bisa zargin Zagon Kasa

 

Wata kungiyar Shugabannin Jam’iyyar NNPP ta zargi Sanata, Rabiu Musa Kwankwaso, da yi wa Jam’iyya laifuffuka da dama.

Legit Hausa ta rawaito cewa, Kwamred Sunday Oginni, ne ke jagorantar kungiyar suna masu zargin dan takararsu da zagon-kasa.

Cikin abubuwan da suke suke zargin Kwankwaso da aikatawa akwai alakarsa da Bola Ahmed Tinubu.

Kungiyar shugabannin jam’iyyar NNPP na reshen jihohi sun kuma bukaci Rabiu Musa Kwankwaso da ya rubuta takardar murabus daga Jam’iyyar.

Leadership Hausa

Leave a Reply