Sabon shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce daga yanzu gwamnatinsa za ta soke batun bayar da tallafin man fetur a ƙasar.
Tinubu ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar, jim kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban ƙasa.
Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta karkata kuɗaɗen ne zuwa wasu ɓangarorin ci gaban ƙasa.
Haka nan sabon shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa za ta zamo mai tuntuɓa da neman shawarwari ba wadda za ta rinƙa ƙaƙaba wa mutane abin da ba su so ba.
Ya ce “Za mu tuntuɓa da tattaunawa amma ba za mu yi ƙarfa-ƙarfa ba.”
A cewarsa zai samar da gwamnati ce wadda za ta wakilci al’umma ba wadda za ta yi mulki kawai ba.
Shugaban ya kuma yaba wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya ce ya yi iyakar bakin ƙoƙarinsa wajen ciyar da ƙasa gaba.
BBC Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.