Skip to content
September 20, 2026
  • About Us
  • Contact Us
  • Personal Information Usage Disclosure
  • Privacy Policy
Albarka Radio

Albarka Radio

Official Website of Albarka Radio, Bauchi.

Primary Menu
  • Home
  • Breaking News
  • Education
  • Health
  • National News
  • Latest News
  • Politics
  • Sports
  • Featured
Light/Dark Button
Listen Live
  • Labarai

Yan Sanda Sun Kama Wata Mace Kan Zargin Kisan Yara Biyu a Toro, Sun Cafke Mutane 16 Bayan Rikicin da Ya Barke

July 24, 2025 2 minutes read

Daga Muhammad Sani Muazu

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Bauchi ta kama wata yarinya mai shekara 19, Esther Gambo, bisa zargin kisan wasu ‘yan mata masu shekara bakwai a kauyen Lemoro, karamar hukumar Toro a jihar Bauchi.

Mai magana da yawun rundunar, CSP Ahmed Wakil, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana cewa wacce ake zargi ta janyo yaran biyu, Khadija Sama’ila da A’isha Dahiru daga Unguwan Sarkin Yaki, da nufin sace jaririyar Nafisa Dahiru.

Wakil ya ce bayan ta samu jaririyar, wacce ake zargin ta kai yaran biyu gonar masara da ke kusa, inda ta yi amfani da adda ta kashe su kafin ta gudu daga wurin. Jami’an ‘yan sanda tare da hadin gwiwar ‘yan kungiyar bijilanti sun samu nasarar gano gawarwakin yaran, tare da ceto jaririyar da aka sace.

Lamarin ya tayar da hankula a yankin, inda matasa suka fito zanga-zanga da tashin hankali, sun kuma kona wasu majami’u tare da yunkurin kona ofishin ‘yan sanda na garin Tulu. Rundunar ta ce an tura karin jami’ai daga Area Command na Toro da sauran sassa domin dakile harin da tabbatar da zaman lafiya.

An kuma kama mutane 16 da ake zargin suna da hannu a rikicin. Sun hada da Abbas Abdullahi (20), Mubarak Auwal (19), Abdullahi Muhammad (19), Dauda Abdullahi (19), Abubakar Sama’ila (18), Abdulmutallib Ibrahim (18), Yazid Auwal (20), Abdulrahman Ibrahim (17), Abdulwahid Sulaiman (17), Salihu Shuaibu (20), Sirajo Halliru (24), Musayib Abdullahi (21), Ibrahim Abubakar (19), Esther Idi (19), Gambo Yakubu (20), da Idi Bitrus (50).

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya nuna damuwa kan yadda al’umma ke daukar doka a hannunsu, inda ya jaddada cewa doka ta yi tanadin hanyoyin magance irin wannan lamari. Ya roki jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da gujewa daukar doka a hannunsu, yana mai tabbatar da cewa rundunar na gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Aliyu ya tabbatar da cewa rundunar ta himmatu wajen tabbatar da adalci ga kowa tare da tabbatar da zaman lafiya a cikin jihar.

Tags: Bauchi State Government Bauchi state police command

Post navigation

Previous: Police Arrest Suspect Over Murder of Two Girls, Sixteen Others Held as Violence Erupts in Toro
Next: YLN, SFCG Trains Community Leaders on Common Ground Approach to Religious Engagement

Related Stories

  • Labarai

Sakon Sakatare Janar Na MDD Na Murnar Fara Azumin Ramadan 2026

February 17, 2026
  • Labarai

Fiye da Mata 100 Sun Kammala Samun Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani a Bauchi Karkashin Shirin Renewed Hope Initiative

July 30, 2025
  • Labarai

“Jami’ar PDP ba ta da alkibla a jihar Bauchi” In ji wani jigo a jam’iyyar APC

July 30, 2025

You May Have Missed

  • News

Nigeria Moves to Unlock $1.2bn ECOWAS Trade Market, Urges Nigerian Businesses to Conquer West African Markets

September 5, 2026
  • Opinion

Nigeria Rejoins World Energy Council – Wunti Takes the Helm

August 8, 2026
  • News

Fathers’ Forum Sparks Change in Bauchi, Men Rally Behind Girls’ Education

June 8, 2026
  • News

Bauchi Mothers Drive Grassroots Push for Girls’ Education and Empowerment

June 8, 2026
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy
Copyright © 2026 Albarka Radio, All rights reserved. | ReviewNews by AF themes.