Labarai

Okonjo-Iweala Ta gana da Shugaba Tinubu Kan Shirin Rage Radadin Wahalhalun Da Yan Najeriya Ke Sha.

 

Darekta-janar ta kungiyar kasuwanci ta duniya WTO, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, tace ganawar da ta yi da shugaban Najeriya Bola Tinubu, na da nufin rage radadin rayuwa ce da yan Najeriya suka tsinci kansu a ciki.

Da dake jawabi ga manema labaru bayan ganawar ta su, Okonjo-Iweala, ta jaddada cewa ziyarar da ta kawo da take ba a hukumance ba, ya maida hankali ne kan yadda za a tagaza wa Najeriya a wannan lokaci na tsananin bukata.

Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa sun tattauna kan muhimman batutuwa da shugaban kasar, game da yadda za a samar da shirye-shirye ga mata da kananan yara dake yankunan karkara wadda a cewarta sune abin ya fi shafa.

Tace sun tattauna kan zuba jari mai dogon zango da zai samar da damarmaki, ciki har da bangaren harhada magunguna.

Ngozi Iweala, ta kuma tabo batun zuba jari a fannin sadarwar zamani da tace yanzu shi ke kan kadamin habaka.

Leave a Reply