Home Labarai WAEC ta riƙe sakamakon ɗalibai 262,803 bisa zargin Satar Jarrabawa

WAEC ta riƙe sakamakon ɗalibai 262,803 bisa zargin Satar Jarrabawa

 

Hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta Afrika ta Yamma, WAEC, ta ce ta riƙe sakamakon jarrabawar ɗalibai dubu 262,803 da su ka rubuta jarrabawar kammala sakandare ta yammacin Afrika, WASSCE.

Patrick Areghan, shugaban ofishin hukumar na kasa ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai domin bayyana fitar da sakamakon jarrabawar na bana.

Ya ce an riƙe sakamakon jarabawar ne dangane da wasu rahotannin da aka samu na satar jarrabawa.

A cewarsa, adadin ya nuna kashi 16.29 cikin 100 na adadin daliban da suka zana jarrabawar.

Ya ce wannan ya yi kasa da kashi 6.54 cikin 100 idan aka kwatanta da kashi 22.83 da aka samu a 2022.

Daily Nigerian Hausa


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.