Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika ECOWAS ta tsayar da ranar da za ta kaddamar da farmaki a Jamhuriyar Nijar da zummar maido da mulkin dimokuradiya ko ta halin-kaka bayan sojojin da suka yi juyin mulki sun ki amincewa da hanyoyin lalama.
Wannan na zuwa ne bayan hafsoshin tsaron Kungiyar Kasashen ECOWAS sun kammala taronsu a wannan Juma’ar a birnin Accra na Ghana, inda suka yanke shawarar daukar matakin soji kan Nijar, yayin da suka ce sojojinsu na ko-ta-kwana na cikin shirin karbar umarnin tafiya filin-daga.
Hafsoshin tsaron sun mayar da hankali kan daukar matakin soji domin maido da hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum kan kujerarsa muddin sojojin da suka yi juyin mulki suka ki amincewa da zaman a teburi domin sulhu.
Ko shakka babu , muddin dukkanin hanyoyi suka gaza, to jajirtattun dakarun kasashen yammacin Afrika da suka hada da sojoji da wani bangare na farar hula, a shirye suke su amsa kira zuwa filin-daga. Inji Abdel-Fatau Musah, Kwamishinan Tsaro da Zaman Lafiya na ECOWAS.
Kodayake, babban jami’in na ECOWAS ya ce, har yanzu suna bai wa diflomasiya dama, kuma zabi ya rage ga sojojin na Nijar.
Taron na kwanaki biyu da ka faro a jiya Alhamis na zuwa ne bayan da jagororin juyin mulkin na Jamhuriyyar Nijar suka yi biris da umarnin kungiyar ECOWAS na ganin sun mayar da mulki ga farar hula tare da sakin shugaba Bazoum da su ke ci gaba da tsare shi.
Rahotanni sun bayyana cewa hafsoshin tsaron na kasashen ECOWAS sun mika wa sojojin Nijar dukkanin tayin ganin an warware matsalar cikin salama ba tare da daukar matakin soji ba.
Ana tsaka da wannan taro ne kuma shugaban Hukumar Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya Volker Turk ya mika bukatar ganin an yi dukkanin mai yiwuwa wajen dawo da mulkin farar hula a kasar ta yankin Sahel lura da wahalhalun da jama’a ke ciki.
RFI HAUSA
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.