Latest:
Labarai

Ma’aikatan Jinya A Jihar Bauchi Zasu Sami Karin Girma Da Kudin Alawus-Alawus

Daga Mubarak Aliyu Kobi

Bangaren kiwon lafiya zai ci gaba da samun fifikon da ake bukata a wa’adi na biyu na Mulkin Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir na jihar Bauchi.

Wannan dai ya yi daidai da yunkurin da gwamnan ya yi a baya na farfado da harkar kiwon lafiya a jihar ciki harda shirya taron koli na masana kiwon lafiya karo na farko, a shekarar 2021 da kuma kokarin da ake yi na samar da ababen more rayuwa da na ma’aikatan kiwon lafiya.

Sabon kwamishinan lafiya da aka nada Dr. Adamu Umar Sambo, ne bayyana hakan a yayin wani takaitaccen bukin mika ragamar jagorancin ma’aikatar lafiya da aka gudanar yau a ma’aikatar da ke Bauchi.

A jawabinsa na farko a matsayin kwamishinan lafiya na jihar Bauchi, Dakta Adamu Umar Sambo ya ce gwamnatin jihar Bauchi za ta ci gaba da baiwa fannin kiwon lafiya fifiko kamar yanda a baya-bayan nan jihar ta dauki karin ma’aikata domin cike gibin wadanda suka yi ritaya daga aiki.

Ya kara da cewa babban kalubalen da ake fuskanta a fannin kiwon lafiya na jihar Bauchi shi ne na karancin ma’aikatan kiwon lafiya, inda ya ba da tabbacin cewa ma’aikatar a karkashin sa zata duba dabaru daban-daban domin samun damar dinke barakar.

Dangane da batun biyan haqqoqin ma’aikata don samun ayyuka masu inganci, Dokta Adamu Umar Sambo ya ce gwamna Bala Muhammad ya yi alkawarin aiwatar da karin girma da sauran haqqoqin Ma’aikata domin hakan zai kara karfafa gwiwar sauran kwararru su zo Bauchi don yin aiki.

Kwamishinan ya nemi goyon baya da hadin kai daga dukkan shugabannin Hukumomi da sassan ofisoshi dake karkashin ma’aikatar domin cimma nasarar abinda aka sa gaba.

Tun da farko a jawabinsa na mika ragamar ma’aikatar, babban sakatare a ma’aikatar kiwon lafiya na jiha, Alhaji Ali Babayo Gamawa ya bayyana cewa ma’aikatar tana da adadin hukumomi bakwai (7) da manyan cibiyoyin kiwon lafiya biyu (2) da kuma Manyan sassa tara (9) kuma dukkansu suna aiki tukuru. cimma burin Ma’aikatar.

Ya bayyana cewa kundin mulkin ma’aikatan ya kunshi bayanin hangen nesa da manufa na Ma’aikatar Lafiya ta Jiha, umarnin doka, tsare-tsare da ayyuka, takaitaccen bayani kan ma’aikata, kayan aiki na ofis, motoci, injina gami da bayanai kan kudaden da aka tura, da wanda suka shigo. shirye-shirye na musamman, lamuni da ayyukan ma’aikatar.

A halin da ake ciki, kungiyar ‘yan jarida masu bada rahotannin kiwon lafiyar al’umma (J4PD), sun taya sabon kwamishinan lafiya na jihar Dakta Adamu Umar Sambo murna.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun ko’odinetan kungiyar Elizabeth Nange Kah, wacce aka rabawa manema labarai a Bauchi ta yi fatan alheri ga kwamishinan.

J4PD ta bayyana burinta na hada kai da ma’aikatar da nufin bayar da gudunmuwar ta domin ingantattun sakamakon kiwon lafiya a jihar Bauchi.

Leave a Reply