Wani sabon bincike da hukumar da ke hana ta’amali da barasa da kwayoyi a Kenya ta Nacada ya nuna cewa adadin masu ta’ammali da wiwi a ƙasar ya ƙaru, wani abu da ake fargaba tsakanin matasa.
Yawan mutanen da ke shan wiwi a Kenya ya ninka sau biyar kamar yadda rahoton Nacada ya bayyana.
Sabbin alƙaluma sun nuna yadda ake samun ƙaruwar masu ta’ammali da kwayoyi a ƙasar.
Sun nuna ƙarancin shekarun da mutane ke fara shan waɗan nan kwayoyi a matakai daban-dabn, kuma yanzu sun nuna yadda ƙananan yara ke fara shan wiwi a ƙananan shekaru.
Alkaluman sun una yadda yara ke fara ta’ammali da kayan shaye-shaye irinsu hodar iblis suna da shekara takwas zuwa sha hudu, yayin da suke fara shan koken a shekara 20.
Rahoton ya nuna aka ɗauki matsalar da muhimmanci tsakanin hukumomi.
BBC Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.