Siyasa

Zan Goyi Bayan Duk Wanda Aka Zaɓa – Wike

Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya ce zai goyi bayan duk wanda ya yi nasara a zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP.

Wike shi ne ɗan takara na ƙarshe wanda ya yi jawabi ga wakilan PDP da za su fitar da gwani tsakanin masu son takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar.

A cikin jawabinsa ya ce PDP na buƙatar irinsa domin kawar da APC daga mulki.

Leave a Reply