News

Dan Firamare Ya Samar Wa Kauyensu Wutan Lantarki

Wani ɗan shekara 14 ya samu kyautuka bayan ya samar wa gidaje da dama wutar lantarki a ƙauyensu na Borana da ke kudancin Habasha wato Ethiopia.

Adan Hussein Dida, wanda ɗan aji na 8 ne a makarantar firamare ta Tula Web, ya ce ya ƙirƙiri lantarkin ce saboda ya rage wa mazauna ƙauyen wahalhalun da suke fama da su kamar rashin hanyoyi da asibitoci da lantarkin kanta.

Ya ƙaddamar da aikin ne daga cikin gidansu, inda ya zuba kashin dabbobi cikin wani rami mai tsawon mita biyu.

Daga nan ne kuma ya samar da wuta ga gidaje takwas. Ya caji kowane gida dala 0.87 duk wata.

Akasarin mazauna ƙauyen makiyaya ne da suka dogara da kiwon dabbobi, amma sun kasance cikin taluci sakamakon fari da Ethiopia ta fuskanta a watannin baya.

‘Yan gidan su Adam sun yi amfani da kuɗin da suke samu daga lantarkin tasa wajen kula da kansu.

“Ina alfahari da abin da na cimma zuwa yanzu, sun ce na tseratar da su daga sayen batiri da kuma cocila.

Yanzu ‘ya’yansu za su iya yin karatu daga gida ba sai sun jira zuwa safiya ba saboda rashin haske,” a cewar Adam.

Malamin Adam mai suna Boru Sora ya ce ɗalibin nasa yana ƙara faɗaɗa aikin nasa zuwa gidaje masu yawa duk da matsalar rashin kyawun hanyoyi da suke fuskanta, wanda ke hana shi samun kayan aiki cikin sauƙi.

“Ɗalibi ne mai fikira. Baya ga samar da lantarkin, ya ƙoƙarta gyaran abubuwa da yawa kamar rediyo da sauran kayan lantarki, har ma da ƙera jirgin da ke tashi tsawon mita 100,” in ji Mista Boru.

Da yawa daga cikin ɗaliban makarantar da Adan ya ba su ƙarfin gwiwa suna ta ƙirƙiro nasu ayyukan.

Burinsa shi ne ya karanta fannin injiniyanci a sabuwar Jami’ar Borana da ke Yebelo.

BBC Hausa ne ta fara buga wannan labarin 

Leave a Reply