Labarai

Ƴan bindiga sun kashe mutum ɗaya da sace mutum 4 a Bauchi

 

Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da cewa yan bindiga sun hallaka mutum ɗaya tare da awun gaba da wasu mutum 3 haɗi da shugabannin al’umma biyu a karamar hukumar Ningi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar SP Ahmed Wakil ne ya tabbatar da hakan a ranar Litinin a Bauchi.

Yace yan bindigan sun kai hari ne a yankin Balma inda suka hallaka mutum ɗaya sannan sukayi garkuwa da wasu mutum uku gamida shugabannin al’umma su biyu a ranar Asabar.

Wakil yace shugabannin al’umman sune Dagacin Balma da mai gundumar Bakutumbu.

Jami’in hulda da jama’an yace rundunar ta samu rahoto ne daga ofishin ta dake Balma cewa yan bindiga sun kai hari kauyen inda suka buɗe wuta babu ƙaƙƙautawa akan mai Uwa da wabi sannan sukayi awun gaba da mai gundumar Alhaji Hussiani Saleh mai shekaru 48.

Wakil yace anyi garkuwa da mai gundumar ne tare da wani Idris Mai Unguwa da wani Ya’u Gandu Maliya mai shekaru 45.

Hakazalika yace yan bindigan sun harbe wani Haruna Jibrin a kayinsa.

Yace da yan sandan suka samu rahoton ne sukayi hanzarin tura jami’an su inda lamarin ya auku kuma sunyi nasarar ceto wanda aka harba har suka kaishi babban asibitin Ningi don samun kulawa kafin daga bisani aka tabbatar ya mutu.

A halin yanzu jami’an yan sanda a karamar hukumar Ningi suna iya bakin kokarin su a cikin daji don ganin an kubutar da sauran mutum biyun da akayi garkuwa dasu da ransu.

Jami’in hulda da jama’an ya bukaci al’umma dasu kasance masu bada bayanai akan duk wani abinda basu yarda da shi ba ko mutanen da basuyi na’am dasu ba wa hukumomin tsaro don daukan mataki.

Leave a Reply