A daidai lokacin da Najeriya ke bikin ranar DimokuraÉiyya na shekara ta 2023, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yace dimokuraÉiyya a Najeriya tana halin ÆaÆanikayi kuma dole yan Najeriya sun haÉa karfi da karfe kafin a ceto ta.
Cikin wata sanarwar data fito ranar Lahadi, dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 25 ga watan Fabrairun shekara ta 2023 yace dole sai wadanda suke kan madafun iko sun daina tsoma baki a sakamakon zaÉe.
Atiku yace ranar dimokuraÉiyyar Najeriya rana ce da za’a auna tsayuwar kasar akan turbar dimokuraÉiyya.
Atiku ya kuma ce akwai sauran aiki a gaba domin farfado da Najeriya cikin hayyacinta na dimokuraÉiyya.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








