Latest:
Labarai

Ƴan Bindiga Sunyi Ajalin Ma’aurata Da Malamin Firamare A Kaduna

 

Ana fargabar cewa wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun kashe wasu ma’aurata da wani malamin makaranta a kauyen Maro da ke Karamar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.

Lamarin kamar yadda wakilinmu ya ruwaito, ya jefa mazauna yankin na Unguwar Dorawar Bakhira cikin firgici, yayin da malamin da lamarin ya rutsa da shi mai suna Mista Sunday Akorh, ya kasance malamin firamare daya tilo a kauyen.

Mazauna sun shaida wa Aminiya cewa, babu wanda aka samu rahoton cewa an yi awon gaba da shi a yayin harin da ’yan ta’addan suka kai da misalin karfe 1:30 na daren Asabar wayewar garin Lahadi.

Wani mazauni kuma jagoran al’umma a yankin, Maigari Ben, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin zantarwarsa da Aminiya a wannan Lahadin.

“Sun kashe wani mutum da matarsa da wani malamin firamare mai suna Mista Sunday Akorh dan asalin Jihar Benuwai.

“Malamin shi kadai ne yake koyarwa a wata makarantar firamare a wannan kauyen. Sai dai babu wanda aka yi garkuwa da shi,” a cewarsa.

Sai dai kokarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin jami’in hulda da rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Manir Hassan ya ci tura a yayin da ba a same shi a wayarsa ba, sannan kuma bai bayar da amsar sakon kar ta kwana da aka tura masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Jaridar Aminiya