Labarai

Ƴan Boko Haram sun kai hari wa tawagar gwamnan Yobe

 

Akalla jami’an tsaron gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni shida ne suka samu rauni yayin wani harin da ‘yan ta’addar Boko Haram suka kai musu a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Gwamna Buni yana Maiduguri tare da manyan baki domin halartar taro karo na 24 a Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) lokacin da lamarin ya faru.

Gwamnan da ‘yan tawagarsa wadanda suka samu rakiyar gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun tafi Abuja a jirgin sama ta sansanin sojin sama da ke Maiduguri.

Majiyoyin leken asiri sun bayyana wa Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa motocin jami’an tsaron da ke cikin ayarin gwamnan, ‘yan ta’addar sun farmake su a babbar hanyar Jakana.

Majiyar ta ce ‘yan ta’addar sun harbe sojojin da ke jagorantar ayarin motocin MRAP da wata motar bindigu da kuma wata motar da ke jigilar ‘yan sanda da jami’an DSS.

“Sai dai sojojin sun mayar da martani ta hanyar bude wuta, lamarin da ya tilasta wa ‘yan ta’addar tserewa, abin takaici, sojoji biyu da suka hada da direba daya da ‘yansanda hudu sun samu raunuka.

“Jami’an tsaro sun dawo Yobe lafiya, yayin da aka kai wadanda suka jikkata asibiti domin kula da lafiyarsu,” in ji Makama.

Jaridar Leadership