Labarai

Ƴan sanda sun kashe ƴan bindiga 4 da kama wasu 13 a Kaduna 

 

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna, ta kashe wasu mutane hudu da ake zargi da garkuwa da mutane tare da cafke wasu 13 a wani samame da ta kai a sassan jihar.

Da yake bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin, mukaddashin kakakin rundunar, ASP Manir Hassan, ya shaida wa manema labarai cewa, an kashe wadanda ake zargin ne a yayin da aka yi artabu a sassa daban-daban a Jihar Kaduna.

Sannan an kama wasu bisa rahotannin sirri da suka samu.

A cewar kakakin ‘yan sandan, daga cikin wadanda ake zargin akwai Auwal Saidu, wani jami’in tsaro mai zaman kansa, wanda ake zargin shi ne ya kitsa sace uban gidansa, sannan ya karbi naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa kafin shi da ‘yan kungiyarsa su sako wanda lamarin ya rutsa da shi.

Wasu daga cikin kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da bindigogi kirar AK-47 guda biyu da babura biyu da kunshin harsashi 15 da kuma buhun tabar wiwi.

Kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Jaridar Aminiya

Leave a Reply