Rundunar âyan sandan Jihar Kaduna ta samu nasarar cafke matasa 13 bisa zargin hannunsu a harkallar ayyukan kungiyar asiri da fashi da makami a garin Zariya.
Jamiâin hulda da jamaâa na rundunar âyan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ne ya sanar da hakan a cikin wata takarda da wakilinmu ya samu a Zariya.
Sanarwar ta ce rundunar âyan sanda da ke Sabon Garin Zariya ce ta cafke wadanda ake zargin.
âWadanda aka cafke din sun tabbatar da kasancewa âyan kungiyar asiri ta (Aiye Confraternity) wadanda suke gudanar da mummunan ayyukan su a manyan makarantu daban-daban.
Bayanai sun ce ababen zargin sun zabi unguwar Graceland a matsayin cibiyar gudanar da ayyukan su.
Sanarwar ta kara da cewa, âda misalin karfe 3 na daren ranar 10 ga watan Satumba ne âyan kungiyar dauke da manyan makamai suka afka unguwar Graceland inda suka rika shiga gidaje suna kwace masu kayayyaki yayin da kuma suka raunata wasu.
âSun kwace wayoyin hannu, da katin cire kudi na ATM da gwala-gwalai da kudade kafin daga bisani suka tsere cikin daji.â
A cewar sanarwar, âdaga nan ne jamiâan rundunar âyan sandan ta bi sahun ababen zargin, inda suka samu nasarar cafke mutum 13 daga cikinsu.â
Jamiâin hulda da jamaâar ya ce yanzu haka wadanda aka kama din suna bai wa âyan sanda hadin kai wajen kokarin kamo sauran ababen zargin da suka arce.
Kwamishinan âyan sanda na Jihar Kaduna, CP Musa Yusuf Garba ya roki iyaye da suka rika sa ido tare da kulawa da irin abokan da âyaâyansu ke muâamulla da su don kaucewa shiga ayyukan taâaddanci.
Kwamishinan âyan sandan wanda ya yaba wa jamiâan rundunar bisa gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.
Kazalika, ya kuma roki alâumma da su rika kokarin sanar da jamiâan bisa duk wani alâamari da ba su gamsu da shi ba.
Jaridar Aminiya
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








