Labarai

Akalla mutane 50 ne suka rasa ransu a rikicin kabilanci a jihar Taraba

 

An sanya dokar hana fita a garin Karim, shalkwatar karamar hukumar Karim Lamido dake jihar Taraba na sa’o’i 24 wanda dokar ta fara aiki daga jiya.

Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ne ya sanya dokar ta-bacin bayan sake barkewar rikicin kabilanci a wasu sassan karamar hukumar, wanda hakan yayi sanadin mutuwar mutane da dama.

Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan jihar, Yusuf Sanda a wata sanarwa da ya fitar, ya ce tuni aka baiwa hukumomin tsaro umarnin tabbatar da bin doka da oda a yankin.

Sanarwar ta kuma umarci dukkan masu unguwanni, da sarakunan gargajiya, da masu ruwa da tsaki na karamar hukumar Karim Lamido da su tabbatar an bi dokar.

Daga karshe sanarwar ta yi kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar an bi doka, kana su hukunta duk wata kungiyoyin ko mutanen da suka karya doka.

Akalla mutane 50 ne aka ruwaito sun rasa ransu yayin da aka kona gidaje da dama a rikicin kabilanci da ya barke a karamar hukumar Karim Lamido a jihar Taraba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Usman Abdullahi, ya ce an fara rikicin ne da sanyin safiyar Asabar din da ta gabata, lokacin da ‘yan kabilar Karimjo suka kai wani mummunan hari kan kabilar Wurkun.

Leave a Reply