Mayakan Boko Haram 82 sun mutu a wani rikicin Æabilanci da ya Éarke a tsakaninsu a yankin Kukawa da ke Jihar Borno.
Majiyoyin tsaro da mazauna yankin Baga da ke kusa da Tafkin Chadi sun ce rikicin Æabilancin ya kunno kai ne bayan Æungiyar ta harbe wasu mayakanta bakwai âyan Æabilar Buduma, har lahira.
Majiyarmu ta ce âSun yi musayar wuta inda aka kashe mayaÆa 82⦠Amma dai rikicin na kabilanci ne.â
Ta ce kwamandan Æungiyar ne ya yanke wa mayaÆan hukuncin harbewa bayan gano shirinsu na miÆa wuya ga sojojin Najeriya.
âKafin su kai ga miÆa wuya ne wasu abokansu da suka ba wa labari suka sanar da kwamandan, ya sa aka daÆile su aka kai su Tsibirin Bukkwaram aka harbe su har lahira.
âWannan ya haifar da rikici tsakanin mayaÆa âyan Æabliun Kanuri, Buduma, Fulani da kuma Hausawa da ke kungiyar.
âKisan ya fusata âyan uwansu âyan Æabilar Buduma, inda suke zargin kwamandan da kama-karya, ganin yadda a baya-bayan nan suke ta rasa mayaÆansu,â in ji majiyar tamu.
Ta ce bayan nan ne Æungiyar ta kira wani zama inda kwamandojinta suka yi ittifaÆi cewa duk wanda ke buÆatar tafiya ya tafi inda ya ga dama.
âAmma Éayansu, Baduma Bakura, Éan ÆabikarBuduma da ya zo taron daga yankin Ali Mandula da ke Nijar ya Æi amincewa.
âYa ce shi ya zo ne domin ya binciki dalilin kashe âyan Æabilarsa, ya kuma yi barazanar harbw duk wanda ya nemi tashi daga wurin.
âHakan ya haifar da zazzafar muhawara, ana cikin haka kuma wani bafulatani ya harbe shi har lahira.
âMayaÆa 82 aka kashe kuma ba za a iya ware âyan Boko Haram ko âyan ISWAP a cikinsu ba. Amma dai rikicin na kabilanci ne,â in ji wata majiyar tsaro.
Majiyar ta ce daga cikin mayaÆan aka kashe a rikicin akwai sanannun fuskokin âyan Boko Haram da a baya suka tsere daga yankunan Baga, Doron Baga da Kukawa zuwa Jamhuriyyar Nijar da ma yankin Sahel.
âA baya sun tsere zuwa tsallaken Tafkin Chadi amma daga baya suka dawo gida kafin rikicin Æabilancin ya yi ajalinsu,â in ji majiyar.
Jaridar Aminiya
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








