Rundanar ‘yan sandan jihar Filato ta gabatar da wata mata mai suna Patient Solomon da ake zargi da sace wata jaririya ‘yar wata 10.
An gabatar da matar ne a gaban jama’a tare da wasu Æarin mutum 27 da ake zargi da aikata munanan laifuka a faÉin jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Okoro Julius, wanda shi ne ya yi holin matar a hwadkwatar ‘yan sanda da ke birnin Jos, ya bayyana cewa rundunar na ci gaba da himma domin tabbatar da an kawo Æarshen ayyukan Éata-gari a gari.
Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa bayan gano jinjirar daga bisani an miÆa ta ga mahaifiyarta.
Mahaifiyar jaririyar mai suna Annabel Geoffrey ta shaida wa manema labarai yadda lamarin ya faru. Inda ta ce “ba ni da masaniyar ta tafi da ‘yata saboda a gida Éaya muke zaune da ita”.
“Bayan an Éauki lokaci ban ga yarinyar ba, sai na kira lambar matar amma kiran ba ya shiga. Daga baya ta kira ni inda ta sanar da ni ta yi tafiya zuwa Legas tare da ‘yata.”
Ta ce bayan haka ne ta kai rahoton lamarin ga jami’an ‘yan sanda. Sai dai wadda ake zargin Patient Solomon ta musanta cewa satar jaririyar ta yi.
A cewarta, ta Éauki yarinyar ne kawai saboda so da Æauna ba wai da nufin cutar da ita ba.
BBC Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








