Labarai

Gwamnatin da ta gabata ce ta jefa Najeriya cikin matsin tattalin arzikin da take ciki a yanzu – Tsohon Sarkin Kano

 

Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya ce gwamnatin da ta gabata ce ta jefa Nijeriya cikin matsin tattalin arzikin da take ciki a yanzu.

Muhammadu Sanusi na II, wanda ya jagoranci Babban Bankin Nijeriya daga 2009 zuwa 2014, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba ta da laifi kan halin da ake ciki a halin yanzu domin kuwa ta gaji matsalolin da ake ciki ne.

Ya bayyana haka ne a wani sakon bidiyo da aka watsa a shafin Instagram a karshen mako.

Ya kara da cewa ya dade yana gargadi kan a gyara matsalolin da ya hango wa kasar amma aka ki gyarawa.

Tsohon shugaban Babban Bankin Nijeriya ya ce duk wanda ya ce gwamnatin Tinubu ce ta jefa kasar cikin matsin da ake ciki a yanzu “ya zalunce ta” saboda ba laifinta ba ne.

Ya ce mutane na ta rubuto masa wasika cewa ana yunwa a kasa amma ya yi gum da bakinsa.

“Ana yunwa, ya kamata a ce mun yi magana amma ba mu yi magana ba, to ni me zan ce? Shekara nawa na yi ina gaya wa mutane cewa wannan wahalar na gabanmu?” in ji Muhammadu Sanusi II.

Ya ce tun lokacin da ya ga an dauki hanyar da ba ta dace ba wurin tafiyar da tattalin arzikin Nijeriya ya san cewa a karshe wahala za a sha.

“Wahalar da ake ciki a yanzu, ta gaba ma ta fi ta,” a cewarsa yana mai karawa da cewa akwai kasashen da a baya suka fuskanci makamancin abin da ke faruwa a Nijeriya.

“Kafin a yi zabe an yi taro a Kaduna, lokacin shi Tinubu yana zaune, na fada na ce duk wani dan siyasa da ya ce muku ba za a sha wahala ba, kada ku zabe shi.

“Su masu cewa na yi magana a yanzu, lokacin da nake magana a kai me suka ce mini? Ce wa aka yi siyasa muke yi, ba ma son gwamnati, muna sukar shugaban kasa,” in ji tsohon gwamnan Babban Bankin na Nijeriya.

Khalifan na Tijjaniya ya ce an shafe shekara takwas ana rayuwa ta karya a Nijeriya inda ya ce an ci ba shi a kasashen waje da cikin gida haka kuma babban bankin kasar ya bayar da bashi na cikin gida kusan naira tiriliyan 30.

“A gwamnatin da ta gabata, sai da ta kai dukkanin nairar da gwamnatin tarayya take samu ba ta biyan kudin ruwa a kan bashi.

“Biyan bashi ya haura kaso dari, wato duk nairar da gwamnatin tarayya ta samu, ta tafi a biyan bashi, sai an ci bashi tukuna a biya kudin ruwa, saboda haka duk abubuwan da aka yi tun daga kan albashi da hidimomi da tituna duk wani sabon bashi aka dauko domin a yi su.

“Saboda haka ba abin da za mu ce wa al’umma sai dai mu ba su hakuri, wadanda Allah ya bai wa hali don Allah ku tausaya wa marasa shi, ba laifinsu ba ne jefa su aka yi,” in ji shi.

Ya ce babu wani abin da zai iya cewa yanzu sai dai ya ba mutane hakuri domin lokacin da ya kamata a saurare shi ba a yi hakan ba.

TRT Afrika

Leave a Reply