Latest:
Labarai

Kiwon lafiya Na Tsada A Nijeriya – Osinbajo

Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce har yanzu fannin kiwon lafiya a Nijeriya a kwai tsada, duk da ɗumbin kasafin kuɗi da ake a fannin kiwon lafiya.

Osinbajo ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis a cikin jawabinsa na musamman a taron ƙaddamar da rahoton manufofin ci gaba mai ɗorewa, SDG, na 3 da 4, wato SDG-3 da SDG-4.

An gudanar da taron ne a ɗakin taro na Banquet Hall dake Abuja.

Osinbajo ya ce dole ne Nijeriya ta ɗinke ɓarakar da ke tsakanin kasafin kiwon lafiya da kuma kuɗaɗen da ake kashewa a kiwon lafiya a faɗin ƙasar.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce rahotannin za su kawo ƙarshen wani dogon aiki da aka fara tun a watan Disambar 2018 a taron ƙara wa juna sani na yankin Afirka kan tsarin SDG a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Osinbajo ya ce da amincewa da ajandar da kuma tsarin SDGs, Najeriya ta tsara wa kanta hangen nesa na kawo karshen talauci da kuma bayar da gudunmowa wajen kare duniya nan da shekarar 2030.

Leave a Reply