Labarai

Sanarwar Dawowar Shirye-Shirye

Shugaban hukumar gudanarwar Albarka Radio, Dauda Muhammad Ciroma ya ce tashar ta dawo watsa shirye shirye bayan wasu gyare gyare da aka yi don inganta ayyukan tashar.

Dauda Ciroma ya bayyana hakan ne a zantawarsa da wakilinmu kan dalilan da yasa tashar ta dauke na tsawon kwanaki biyu.

Ya ce ba sabon abu bane yin gyare gyare a gidajen Radio, domin hakan na taimakawa wajen inganta shirye shirye da labaran tashar.

Ya kuma mika godiya wa daukacin al’umar jihar Bauchi bisa nuna damuwa da fahimta da suka yi a lokacin katsewar tashar.

Leave a Reply