Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya sha alwashin hada kan al’ummar kasar da ta tsunduma cikin matsalar rarrabuwar kai bayan da aka sake zabensa a karo na biyu.
Da yake jawabin godiya ga dumbin magoya bayansa a kusa da Hasumiyar Eiffel da ke birnin Paris a daren Lahadi, shugaba Macron ya sha alwashin dinke barakar dake tsakanin ’yan kasar da suka rarrabu.
Macron, ya lashe zaben ne dai da kusan kaso 59 na jimullar kuri’un da aka kada, yayin da abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen, ta samu kashi 41.46 kamar yadda sakamakon karshe daga Ma’aikatar Cikin Gidan Kasar ya nuna.
Macron ya kafa tarihin zama Shugaban Faransa na farko cikin shekara 20 da aka zaba don yin wa’adi na biyu a jere.
Kazalika nasarar tasa ta faranta ran mutane da dama a nahiyar turai, ganin cewa an taka wa masu tsattsauran ra’ayi birki a kokarinsu na karbe mulki a kasar da ke da muhimmanci a cikin kungiyar Tarayyar Turai.
Sai dai a wannan nasarar da ya samu a kan masu tsatsauran ra’ayi, tazarar ba ta da yawa ba sosai idan aka kwatanta da arangamar da suka yi a 2017.
Macron, a wancan lokacin ya lashe kashi 66 na jimillar kuri’un da aka kada, kuma sakamakon da Le Pen ta samu yanzu shine mafi armashi da masu tsattsauran ra’ayi suka taba samu a kasar.
To sai dai akwai gagarumin aiki a gaban Emmanuel Macron a wannan wa’adi na biyu da ya samu wanda ya hada da shirin tinkarar zaben Majalisar Dokokin Kasar a watan Yuni mai zuwa.
Inda ake sa ran Macron ya samu rinjayen da zai iya aiwatar da manufofinsa, da kuma batun neman mafita game da mamayar da Rasha ta ke yi wa Ukraine.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.