Latest:
Labarai

An Ciro Gawar Mutum Biyu Da Gini Ya Danne A Jahar Legas

An zaƙulo gawar mutum biyu daga cikin shida da ɓaraguzan gini suka danne bayan wani bene mai hawa bakwai ya rikito a birnin Legas da ke kudancin Najeriya.

Sakataren hukumar agajin gaggawa ta LASEMA, Dr Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce an gano gawar mutum biyu kuma an fito da su.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da aikin zaƙulo sauran mutum huɗun da ake zaton ginin ya danne.

LASEMA ta ce ginin, wanda ke kan Titin Oba Idowu Oniru, ya ritsa da mutum shida bayan faɗowarsa a cikin dare wayewar garin Lahadi.

Leave a Reply