Daga Fa’izu Muhammed Magaji
Rundunar Yan sandan jihar Bauchi ta gurfanar da wani matashi da ake zarginsa da shiga makaranta rariya da kunce fankan sama a ciki makaranta.
A cewar Dan sanda mai gabatar da kara a gaban kotun Rabiu Ibrahim sarki a wata rana cikin watan 05 din shekara 23, wani mai suna Abdullahi H Sambo kana shugaban makaranta rariya dake nan bauchi, ya kawo rehoto offishin yan sanda akan cewa wasu matasa bata gari, wanda ba’asan ko su wayeba, suka shiga cikin makarantar suke balle musu taga guda biyar, wanda kudinsa yakai kimanin naira 25, da kofa wanda kudinsa yakai kimanin naira 17, sai alli, wanda kudinsa yakai naira dubu 5, da kuma littafin ajiye bayanai na makarantar, da sauran wasu kayayyakin makarantar, wanda dukkanin kudin da ake tsammanin kudin kayan da aka sace yakai naira dubu 48.
Bayan kawo wanna rehoto ne, Dan sandan yace a ranar 05-08-23, wanda ake zargi mai suna Abubakar Husaini aka masaleli ya shiga cikin makarantar ya balle fankan sama, wanda kudin wanna fankan yakai kimanin naira dubu 20, bayan cuka hannu da jami’an tsaro na makarantar sukayi, suka garzayo da wanda ake zargi zuwa offishin yan sanda.
Kana Dan sanda R I Sarki yace aikata hakan in ya tabbata laifine daya sabawa kudin laifuffuka da hukumce hukumcensu sashi na 186,150, na tsarin dokan penal.
Bayan Dan sanda ya gama karanta wa kotu laifin Abubakar Husaini, alkalin kotun yake tambayan matashin, inda matashin ya kada baki yace eh anyi hakan, sai dae shi wanna fankan kawai ya balle a makarantan.
Alkalin kotun ya juya kan Dan sanda yace masa kaji wanda ake zargi ya amsa wasu laifin, sai dae wasu laifin bai amsa suba, Dan sanda yace tunda wanna kotun, kotun shari’ar musulumcin ne, toh yana rokon kotun da tabayar wa matashin rantsuwa akan kayayyakin da bai sace ba, kan yana rokon kotu mai adalci data basu wata rana don ayi ma wanda ake zargi hukumci akan laifin da ya amsa.
Alkalin kotun Barr Muktar Adamu Bello Damban yace kotu ta bayar wa matashin wata rana don yaje ya yi tunani akan rantsuwar da zaiyi akan laifin da yake musu bai sace ba, kotu ta daga zuwa ranar 14-08-23.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.