Labarai

An Kona Dillalan Kwaya 3 Da Ransu A Afrika Ta Kudu

Ƴan sanda a Afrika Ta Kudu sun ce suna cikin halin ko-ta-kwana bayan wani lamari da ya faru inda aka ƙona wasu mutum uku da ransu a cikin gida.

Rahotanni sun ce jama’ar gari ne suka ƙona mutanen bisa zarginsu da safara da dillancin miyagun ƙwayoyi.

Waɗanda ake zargin suna tsakanin shekarun 22 ne zuwa 36, kamar yadda ƴan sandan ƙasar suka bayyana.

Waɗanda aka ƙona ɗin an ce sun caka wuƙa da kuma raunata waɗanda suka kai musu harin, amma an tura su cikin gida inda aka cinna wa gidan wuta suka ƙone a ciki.

Babu wanda aka kama kan wannan lamari.

Leave a Reply