Labarai

Gwamnatin Jihar Kano Ta Soke Lasisin Duk Makarantu Masu Zaman Kansu A jihar

 

Gwamnatin Kano ta sanar da soke lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu da ke fadin jihar.

Jaridar Kano Focus ta ruwaito cewa mai bawa gwamna shawara na musamman kan makarantu masu zaman kansu, Alhaji Baba Abubakar Umar ya sanar da hakan ne a wani taro da ya yi da mamallakan makarantun a ranar Asabar.

Umar ya ce, ana sa ran dukkan makarantun za su karbi sabon fom din rajista domin sabunta lasisinsu

Mashawarcin na musamman ya nanata kudirin gwamnatin jihar na tsaftace ayyukan makarantu masu zaman kansu tare da tabbatar da bin tsari da ka’idoji.

Ya kuma bukaci masu makarantun da su biya kashi 10 na harajin gwamnati da ya rataya a wuyansu a daidai lokacin da ya kamata domin tabbatar da ci gaban bangaren ilimi a jihar.

Umar ya kuma ce kar a dauki wannan lamari na dawo da tsarin kula da makarantu masu zaman kansu a matsayin barazana ba, domin kuwa ba shi da niyyar cin zarafin kowa.

Ya kuma jaddada matsayinsa na daukar matakan da suka dace kan duk wata makaranta mai zaman kanta da aka samu ta bijirewa wannan ka’ida.

Ya bayyana cewa an samar da wata manhaja da za ta magance duk wata matsala daga gwamnati, masu makarantu, iyaye da ma masu neman aiki a makarantu masu zaman kansu.

Jami’in gwamnatin ya kuma ba wa iyaye tabbacin kare muradin su da na ’ya’yansu.

Da yake jawabi a madadin masu makarantun, shugaban kungiyar mamallaka makarantu masu zaman kansu na kasa reshen Jihar Kano, Alhaji Muhammad Malam Adamu, ya bayyana matakin a matsayin abin a yaba domin zai kara bunkasa harkar ilimi a jihar.

Jaridar Aminiya

Leave a Reply