Labarai

An lakaɗawa Alkali duka a Gombe

 

Wasu bata-gari sun sassari alkalin wata Babbar Kotu ta III (UAC III) da ke Gombe Ayuba Buba Dallas, da wasu mutum uku a garin Degri da ke Karamar Hukumar Balanga ta Jihar Gombe.

Wakilinmu ya ruwaito cewa sai da maharan suka yi wa alkalin da sauran mutane ukun kudan kawo wuka sannan suka sassare su.

Sauran wadanda lamarin ya shafa sun hada da lauya mai suna Barista Usman Yahya da wani ma’aikacin kotu.

Wata majiya ta ce wasu mutanen kauyen ne suka kai wa alkalin hari a lokacin da suke kokarin ganin sun warware matsalar rikicin wani fili.

Majiyar ta ce alkalin ya sha bugu ne daga kauyawan da ba a gane su wane ne ba a lokacin da shi da ma’aikatan kotun suka je duba filin a garin na Degri.

Wasu bayanai na alakanta harin da zargin da wasu ke wa ma’aikatan kotun da neman yin rashin adalci a takaddamar filin.

One thought on “An lakaɗawa Alkali duka a Gombe

Comments are closed.