Latest:
LabaraiSiyasa

An Rantsar Da Shuwagabannin Ƙungiyar Goyon Bayan Osinbanjo Na Ƙasa

Ƙungiyar Arewa Youths Support Professor Yemi Osibanjo For President 2023 ta rantsar da Shuwagabannin ta na ƙasa a Kaduna. Dakta Maina Isma’il Abdullahi Gimba shi ne Shugaban Ƙungiyar na ƙasa.

Taron ya gudana ne a ranar Talatar da ta gabata a jihar Kaduna

A jawabinta ga manema labarai Hajiya Hafsat Waiwaye, wacce ita ce mai bada shawara a ƙungiyar ta ce, “Mun zauna da Osinbanjo kuma ya yi mana alƙawarin idan ya zama shugaban ƙasa Gwamnatinsa za ta kula da mata da matasa.”

Har ila yau, matasan ƙungiyar sun ce, Osinbanjo zai farfaɗo da Kamfanoni Arewa, kuma su na sa ran zai kawo masu ƙarshen barace-barace da matsalar tsaro, kuma zai farfaɗo da tattalin arzikin zuwa yankin.

Leave a Reply