Labarai

Gobara Ta Cinye Kayayyakin Fiye Da Naira Miliyan 70 A Tsohuwar Kasuwar Gombe

 

 

Da tsakar daren ranar Larabar da ta gabata ce, gobara ta afku a tsohuwar kasuwar Gombe, wacce ake zargin wasu gungun ‘yan fashi da makami ne suka haddasa, da ta yi sanadin asarar dimbin dukiyar da aka kiyasta ta haura Naira miliyan 70.

 

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 12 na dare a layin teloli, inda wutar ta mamaye shaguna kusan 20 tare da lalata su. Baya ga kadarorin da aka yi asara, ‘yan fashin sun kuma sace kayayyaki na miiyoyin nairori daga shagunan da lamarin ya shafa.

Daya daga cikin masu shagunan da lamarin ya shafa, Aminu Abdulrahman, ya bayyana cewa an buga masa waya ne da karfe 1:00 na dare, inda aka sanar da shi ibtila’in wutar.

Ya ce ya yi asarar kekuna dinki guda goma da wasu kayayyaki masu daraja, wadanda aka kiyasta kudinsu ya kai naira miliyan biyu da dubu dari biyar.

Shi ma wani mai shago a tsohuwar kasuwar Gombe Sani Idris, ya bayyana abin da ya faru cikin bakin ciki, inda ya ce shi ma ya samu kiran waya ne da misalin karfe 1 na da re. Ya ce ya yi asarar kekunan dinki biyar da na saka da sauran kayayyaki wanda kudadensu ya kai na naira 800,000.

Wadanda lamarin ya shafa sun yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni su kai wa wadanda ibtila’in ya shafa dauki gaggawa ddaga wannan mawuyacin hali.

Da yake tsokaci kan wannan mummunan lamari, shugaban kungiyar teloli reshen tsohuwar Kasuwar Gombe, Abu Safwan Muhammad Tukur, ya bayyana kaduwa da alhini kan lamarin.

Ya ce mambobinsu sun yi asarar dukiya mai dimbin yawa da suka hada da kekunan dinki da sauran kayayyaki da kudinsu ya haura naira miliyan 70.

Abu Safwan ya bukaci hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Gombe ta gaggauta kai musu dauki tare da ba da tallafi ga masu shagunan da abin ya shafa.

Jaridar Leadership

Leave a Reply