Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bada umarnin tube rawanin Sarkin Kurayen Katsina kuma Hakimin Kuraye a ƙaramar hukumar Charanci bisa zarginsa da ɗaura Aure da mai cutar Kanjamau.
Hakan na kunshe ne acikin wasu takardun sanarwa biyu da aka fitar daga ofishin gwamna da kuma masarautar Katsina.
Takardar farko da masarautar Katsina ta tabbatar da korarar Hakimin wanda sakataren masarautar Katsina Alhaji Bello Mamman Ifo ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa, an yi wa sarkin Kurayen Katsina, Alhaji Abubakar Al’adu ritaya bisa umarni da masarautar ta samu daga ofishin sakataren gwamnatin jihar Katsina, Barista Abdullahi Garba Faskari.
Sanarwar ta kara da cewa, bisa umarnin na gwamnatin jihar, Masarautar Katsina ta yi wa sarkin Kurayen Katsina kuma Hakimin Kuraye ritaya daga muƙaminsa a ranar Litinin 18/09/2023.
Jim kadan bayan wannan sanarwar ta fadar mai martaba sarkin Katsina, sai kuma ofishin sakataren Gwamnatin jihar Katsina ya fitar da wata sanarwar ga manema labarai wanda daraktan yaɗa labarai Abdullahi Aliyu ya sanya wa hannu akan rabawa manema labarai a Katsina.
Sanarwar ta ofishin sakataren Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa, bisa la’akari da shawarwarin masarautar Katsina, gwamnati ta amince da yi wa sarkin Kurayen Katsina Hakimin Kuraye, Alhaji Abubakar Abdullahi Amadu ritaya daga muƙaminsa na Hakimi.
“An tube rawanin Hakimin ne bayan gudanar da bincike kan korafin da aka shigar, ana zargin Hakimin da daura Aure da wani mai cutar Kanjamau.
“Sakamakon binciken ya tabbatar da zargin da ake yi wa tubabben Hakimin.” inji sanarwar.
Jaridar Leadership
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.