Latest:
Labarai

UNGA: Tinubu ya bukaci a hukunta masu sace ma’adanan Afirka

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi kira ga kasashen duniya su hukunta kamfanoni da daidaikun mutane da ke da hannu wurin sace ma’adinan Afirka da safarar makamai da kuma daukar nauyin ta’addanci.

Ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a wurin Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya na 78 da ake yi a birnin New York na Amurka da ranar Laraba da sanyin safiya a agogon Nijeriya.

A cewarsa abu mafi muhimmanci ga aminci da hadin kan duniya shi ne a kare wuraren da Allah ya huwacewa albarkatun ma’adinai a Afirka daga masu barnatar da su da kuma rikice-rikice.

“Yawancin wadanda wurare sun fada cikin kunci kuma ana ci-da-guminsu. Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ta kwashe shekaru aru-aru tana cikin wahala, duk da kasancewar Majalisar Dinkin Duniya a kasar. Duniya ce ta fi cin albarkacin DRC, amma abin da ake ba ta kalilan ne,” in ji Shugaba Tinubu kamar yadda sanarwar da kakakinsa Ajuri Ngelale ya fitar ke cewa.

Ya kara da cewa: “Kamfanonin kasashen duniya da ke taimaka wa masu aikata laifuka na cikin gida, wadanda ke neman zama manyan masu laifuka, sun jefa dubban mutanenmu cikin bauta ta yadda suke hako musu zinare da sauran ma’adinai ta haramtacciyar hanya.”

Shugaba Tinubu ya ce ana amfani da biliyoyin dala da ake samu ta wannan haramtacciyar hanya wajen haddasa husuma, yana mai cewa “idan ba a dauki mataki ba, za su yi barazana ga zaman lafiyar kasa.”

Shugaba Tinubu ya ce ganin girman yadda ake yi wa Afirka rashin adalci wajen sace ma’adinanta ya sa mutanen nahiyar na tambaya anya ba da gangan hakan ke faruwa ba.

Dole ne manyan kamfanoni da mutanen manyan kasashe su daina barnatar da albarkatun kasar Afirka “nan-take,” in ji Shugaba Tinubu.

TRT Afrika

Leave a Reply