Labarai

Gwamnan Matawalle Ya Sanya Hanu A Kan Dokar Muggan Laifuka

Published by Abdullahi Yahaya

Gwamnan Jihar Zamfara  Bello Matawalle ya sanya hannu kan dokar hukunta dukkan wadanda hukumomin jihar suka kama suna aikata laifuka kamar na kora shanu, satar mutane da shiga kungiyoyin asiri da kuma aikata ta’addanci.

Tun a jiya Litinin dai majalisar jihar ta mika kudurin dokar bayan wani zama na musaman da dukkan ‘yan majalisar suka halarta.

Dokar ta tanadi hukuncin kisa ga dukkan wanda aka samu sun aikata wadannan laifukan.

An amince da kudurin dokar ne yayin wani zama da dukkan ‘yan majalisar Jihar Zamfara suka halarta Gusau babban birnin Jihar.

Matsalar tsaro a yankin yayi mummunan tasiri ga jama’ar jihar, wadda ta hada da bayyanar ‘yan bindiga da barayin daji da masu satar mutane domin karbar kudin fansa.

Hakazalika ana fama da masu sanar da wadannan miyagun mutanen halin da mazauna garuruwa da kauyukan jihar ke ciki domin su kai musu hare-hare.

Lamarin ya kai matsayar da tilas jama’a ke kauracewa muhallansu zuwa wasu yankunan domin neman mafaka.

Manoma ba sa iya zuwa gonakinsu, kuma wasu kauyukan da garuruwan sun zama tamkar kufai.

Wani cikin misalan irin tabarbarewar da al’amura suka yi, a baya-bayan nan, shi ne yadda ‘yan bindiga suka addabi garin Mada, kuma suka tarwatsa mazauna garin duk da cewa yana kusa da Gusau babban birnin jihar ne.

Akwai tambayoyi masu dama a zukatan ‘yan Najeriya, musamman kan tasirin da wadannan tagwayen matakan da gwmantin Zamfara ta dauka domin kokarin magance matsalar tsaro – na farko yin kira ga jama’ar jihar da su mallaki makamai domin kare kansu, da kuma kafa wannan dokar da gwamnan jihar ya sanya wa hannu.

About the author

Abdullahi Yahaya

Seasoned Blogger. Software Developer. Web Designer & Developer. Cybersecurity Expert. Database Engineer. IT Enthusiast.

Leave a Comment